An hallaka wani Bajamushe a Kano

Gidan da aka rushe a Kano
Image caption Gidan da aka rushe a Kano

Rundunar tsaron hadin gwiwa a Kano da ke arewacin Nigeria, ta tabbatar da mutuwar wani dan kasar Jamus da aka sace jihar da kuma wasu mutane biyar a wata musayar wuta da aka yi da safiyar yau a birnin.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar dazu, tace, mutumin ya mutu ne bayan wani samame da ta kai wani wuri da ta ke zargin cewa maboyar wasu jagororin mutanen ne da ke kai hare hare a birnin.

A watan Janairun wannan shekarar ne dai mutanan suka sace Bajamushen wanda injiniya ne dake aiki a kamfanin gine-gine na Dantata and Sawoe, inda tun daga wannan lokaci su ke garkuwa da shi a birninna Kano.

Yanzu haka dai jami'an tsaron rushe gidan da lamarin ya faru.

A wani labarin kuma rundunar 'yan sanda a jihar kwara dake arewacin Najeriya ta ce an sace wani dan kasar Italiya a jihar. Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da halin da yake ciki, amma 'yan sanda sunce suna binciken al'amarin.

Haka na zuwa ne 'yan watanni bayan mutuwar wani dan Italiya Franco Lamolinara da wani dan Burtaniya, Chris McManus a Jihar Sokoto wajen cetonsu bayan an sace su a jihar Sokoto.

Mutanen biyu an sace su ne a jihar Kebbi dake arewacin kasar a shekarar 2011.

Karin bayani