Isra'ila ta mika gawarwakin Palasdinawa

Gawarwakin Palasdinawa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gawarwakin Palasdinawa

Hukumar mulkin Palasdinawa ta karbi gawakin Palasdinawa fiye da 90 da aka kashe a lokacin da suke kai hare-hare a kan Isra'ila.

Gawarwakin sun hada da na 'yan kunar bakin- wake, da na masu fafutuka da suka hallaka a hare-haren da suka kai wa Isra'ilar a 1975.

Palasdinawa sun yi ta bushe-bushe da kade-kade na girmama mamatan a lokacin da ake mika gawarwakin nasu.

Isra'ila dai ta ce ta mika gawakin ne domin karfafa yarda tsakanin bangarorin biyu.

Matakin mika gawarwakin dai yana a matsayin wani bangare ne na wata 'yarjejeniya da aka cimma a farkon wannan watan, domin kawo karshen yajin cin abincin da daruruwan fursunonin Palasdinawa ke yi a gidajen kurkukun Isra'ila.

Za a dai gudanar da wani taron addu'o'i na musamman domin binne gawarwakin.

Karin bayani