Taro kan Somaliya zai duba hanyoyin gina kasar

Hakkin mallakar hoto s
Image caption Soji a Somaliya

'Yan siysar Somalia, dattawa da 'yan kasuwa za su hadu da Shugabannin kasashen duniya a birnin Istambul.

Taron da da za a fara nan gaba a yau zai yi laluben hanyoyin kawo karshen yamutsin da aka shafe shekaru ashirin ana yi a kasar Somalia.

Turkiyya tana son amfani da kyakkyawar fatan da take wa Somaliar da wata ziyara da Prime Ministan Turkiyyar Recep Tayyip Erdogan ya kai bara a kasar ta hanyar kaddamad da zirga-zirgar jiragen saman ta zuwa kasar.

To, amma masu sharhi kan al'amurra sun yi nunin cewa tarukkan kasashen duniya da aka gudanar a baya-bayan nan ba su yi wani abin azo a gani ba ta fuskar warware matsalolin kasar ta Somalia.

Karin bayani