Amurka na kamun kafar Rasha

Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta gargadi Rasha cewa manufarta game da Syria tana taimakawa wajen jefa kasar cikin yakin basasa.

A wani jawabi da ta yiwa wasu dalibai a birnin Copenhagen na Denmark, Mrs Clinton ta ce gwamnatin Syria za ta iya sauraren Rasha, abun da ya sa ta ke matsa lamba a kan Rashar domin ta tsaurara matsayinta a kan gwamnatin Syriar.

Rasha dai tana goyon bayan shirin wanzar da zaman lafiya na wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Syriar, Kofi Annan, amma ta hau kujerar na ki sau 2 kan wasu kudurori kwamitin sulhu na Majalisar Dikin Duniyar dake yin Allah Waddai da gwamnatin kasar ta Syria.

Daya daga cikin kudurorin yayi kira ne ga shugaba Assad da ya sauka daga kan karagar mulki.

Amurka dai na kokarin ta nuna cewa goyon bayan da Rasha ke baiwa gwamantin Basher Al-Assad ne ke kara dagula matsalar Syriar.

Sakatariyar harkokin wajen Amurkan Hilary Clinton, ta gayawa dalibai a Copenhagen cewa, koda yake kasashen duniya na ta kara kiran da ayi amfani da karfin soji don magance matsalar Syrian, kamar yadda akayi a Libyan, Rasha ba za ta bada hadin kai ba.

To a can Syrian dai gwamnatin na ta kokarin tsame hannunta daga batun kashe-kashen da akayi a Houla, wanda ya harzuka kasashen duniya. Gwamnatin ta fitar da rahoton farko na binciken da tayi akan batun.

Kuma shugaban kwamitin da ya yi binciken, Birgadiya-Janar Qassem Jamal Suleiman, yace wadanda suka yi kashe-kashen sunyi sune don su nunawa duniya cewa kasar na neman fadawa cikin yakin basasa.

Karin bayani