An samu mutane hudu da laifin shirya kai hari a Denmark

Hakkin mallakar hoto AP

Wata kotu a Denmark ta samu wasu mutane hudu da laifin shirya makirci da nufin kai hari a kan wani gidan jarida wanda ya wallafa hotunan Annabi Muhammadu (SAW) a shekarar 2005.

An yankewa mutanen, wadanda ukku daga cikinsu mutanen Sweden ne 'yan asalin Gabas ta Tsakiya dayan kuma dan Tunisia, hukuncin zaman kaso na shekaru goma sha biyu.

Kotun ta kuma ba da umurnin korarsu daga Denmark bayan sun kammala zaman kason.

A cewar masu shigar da kara mutanen sun shirya yin harbin kan mai-uwa-da-wabi ne a ofishin jaridar Jyllands-Posten da ke Copenhagen.