An ji karar harbe harbe a Tripoli

Hakkin mallakar hoto Reuters

An ji karar harbin bindiga a babban filin jirgin sama na Libya, wanda ke kusa da Tripoli, babban birnin kasar, bayan da wasu mayakan sa-kai suka shiga filin sannan suka hana tashi ko saukar jirage.

Wakiliyar BBC a birnin na Tripoli ta ce ta ga jiragen sama guda shida wadanda a karkashinsu aka girke wasu manyan motoci dauke bindigogi.

Mayakan sa-kan dai na bukatar a saki daya daga cikin shugabanninsu ne wanda suka ce an kama kwanaki biyu da suka gabata.