Anyi kashe-kashe a Jihar Adamawa

Rahotanni daga arewan Nijeriya na cewa ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma 'yan kabilar Bachama dake kan iyakar jihohin Adamawa da Taraba.

Kungiyar Fulani makiyaya ta Mitetti Allah a Nijeriya ta yi ikirarin cewa an kashe mata mutane kimanin goma sha bakwai cikin 'yan kwanakin nan a lamura na kisan dauki dai-dai.

Rahotanni dai na cewa lamarin baya-bayan nan na ramuwar gayya ne.

Hukumomin tsaro dai sun bayyana cewa sun tsaurara matakan tsaro a yankunan da lamarin ya shafa kuma tuni suka shawo kan rigimar.