Ana kai hare-hare a Syria

Hakkin mallakar hoto AP

Birnin Homs na kasar Syria na fuskantar sabbin hare-hare daga dakarun gwamnati.

Wani wakilin ganau yace BBC ya ce ya ji sautin jirgin sama mara matuki da yace sojojin Syria na amfani da su don gano wuraren da za su kai hari kafin su fara luguden wuta.

Wakilin na BBC ya kuma ce an tsananta kai hari a wani yanki na kewayen tsohon birnin Homs, inda tashin bakin hayaki kan biyo bayan karar saukar rokoki.

Har yanzu masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya ba su samu damar shiga yankin don ganin halin da ake ciki ba.

Karin bayani