Aung San Suu Kyi ta yi kira ga masu zuba Jari

Aung San Suu Kyi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabar 'yan adawar Burma, Aung San Suu Kyi

Shugabar 'yan adawa a kasar Burma, Aung San Suu Kyi ta yi jawabi ga shugabannin 'yan kasuwa a Bangkok, a ziyarar da ta kai kasar waje a karon farko cikin shekaru ashirin.

Ta yi kira a gare su da su tallafawa kasar ta Burma ta hanyar saka jari a fannin ilmi da kuma samar da ayyukan yi.

Suu Kyi ta yi jawabin ne a taron tattalin arziki na duniya kan Gabashin Asia, inda ta roki masu zuba jarin da cewa su kuma taimaka wa al'ummar kasar Burma.

Ita dai Aung San Suu Kyi wacce ta shafe shekaru goma sha biyar cikin daurin talala, ta jaddada bukatar da ke akwai na yaki da cin hanci da rashawa dama nuna wariya a kasar ta Burma.