An dora laifin kisa a Houla kan 'yan tawaye

Susan Rice Hakkin mallakar hoto r
Image caption Jakadar Amurka a Majalisar Dinkiin Duniya

Kwamitin binciken kisan gillar da aka yiwa fareren hula sama da dari a birnin Houla na kasar Syria, ya dora alhakin kan 'yan tawaye.

Shugaban kwamitin Janar Qasem Jamal Suleiman ya bayyana cewa wadanda lamarin ya rutsa da su iyalai ne masu son zaman lafiya da suka kauracewa shiga zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar.

Sai dai kuma jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice ta yi watsi da adadin wadanda aka hallaka da kasar Syria ta bayar a matsayin karya tsagwaron ta.

Ta kuma soki kasar Rasha game da rahoton da wata kungiyar kare hakkin bil'adama da kuma jakadun kasashen yamma suka bayar cewa wani jirgin ruwan kasar ya shiga da makamai kasar Syria cikin yan kwanakin nan.