Najeriya ta kara farashin wutar lantarki.

Tashar wutar lantarki ta Najeriya Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tashar samar da wutar lantarki ta Najeriya

Hukumomin Nijeriya sun yi karin farashin wutar lantarki , da nufin janyo hankalin masu zuba jari a bangaren wutar lantarkin kasar.

Wannan dai, yazo ne a daidai lokacin da jama'ar kasar ke kokawa da karancin wutar lantarkin.

Ko da yake dai, mahukunta na ikirarin cewa karin ba zai shafi talakawa ba, illa manyan kamfanoni da masu hannu da shuni, to amma masana tatttalin arziki na ganin cewa yanzu ne ma talakawa zasu fi dandana kudar farashin wutar lantarkin.