An ceto wasu da aka sace a Afghanistan

afghanistan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun Birtaniya a Afghanistan

Dakarun kasashen yamma sun ceto wasu ma'aikatan agaji guda hudu-biyu daga cikinsu mata - wadanda aka sace watan Mayu.

Janar Adrian Bradshaw, jagoran dakarun Biritaniya a Afghanistan, ya ce sai da aka dan fafata kafin a samu ceto su.

Bradshwa ya ce, "Sai da aka dan kabsa, amma ina iya tabbatar da cewa wasu daga cikin wadanda suka sace mutanen, ko dai an kashe su ko kuma an raunata su."

An kashe mutane biyar daga cikin wadanda suka sace sun, a lardin Badakhshan.

Matan, 'yar Biritaniya ce da 'yar Kenya, wadanda a halin yanzu suke birnin Kabul.

Karin bayani