Ana zanga zanga a Masar akan hukuncin kotu

masar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga zanga sun ce an yiwa Mubarak sassauci

Dubun-dubatar masu zanga-zanga ne ke ci gaba da kwarara zuwa dandalin Tahrir a birnin Alkahira na Masar.

Suna nuna adawa ne da hukuncin da aka yanke wa tsohon shugaban Masar din, Husni Mubarak.

Masu zangar-zangar dai suna cewa ne an yi wa hambarraren shugaban sassauci a wannan hukuncin da kotu ta yanke a yau.

Hukuncin da aka yankewa tsohon shugaban kasar Masar, Husni Mubarak ya kara janyo rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan kasar ta Masar .

Kotun ta ce Mubarak zai shafe karashen rayuwarsa ne a gidan kaso amma kuma ta wanke sauran mukarrabansa wanda suka aikata abubuwa a bisa umurnin daya basu.

Wannan ya janyo wasu 'yan kasar na zargin cewar akwai wata manakisa a bangaren shari'ar kasar, shi yasa aka wanke wasu daga cikin na hannun dama Mubarak din.

A birni na biyu mafi girma a Masar din wato Alexandria na kuwa kiraye kiraye aka yita yi na cewar, kamata yayi a yankewa Mubarak hukunci kisa.

Haka zalika an gudanar da zanga-zanga a biranen Suez da kuma Mansoura.

Nan da makwanni biyu ne za a gudanar da zaben shugaba kasar a Masar din, kuma daya daga cikin 'yan takarar wato Ahmed Shafiq wanda tsohon na hannun daman Mubarak ne, ya yi kira a mutunta hukuncin na koti, a yayinda shi kuma dan takarar Muslim Brotherhood Mohamed Morsi yace an yi matukar sassauci a wajen yanke hukuncin.

Karin bayani