Mutane goma sun mutu a tashin hankali a Lebanon

Lebaonon Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Sojoji na kokarin kwantar da tarzoma a Lebanon

Tashin hankali ya barke a birnin Tripoli na kasar Lebanon dake makwabtaka da kasar Syria tsakanin kungiyoyin dake hamayya da juna.

Akalla mutane goma ne aka bada sanarwar sun rasu sakamakon tashin hankalin.

Birnin Tripoli mai cike da musulmi ma biya akidar Sunna, yana kuma da wasu 'yan Alawite wadanda keda rinjaye a kasar Syria.

Wakilin BBC a Beirut ya ce wannan ne fada mafi muni tsakanin bangarorin biyu a Tripoli, tun bayan da aka soma tashin hankali a kasar Syria.

A lokacin arangamar dai, masu goyon bayan Shugaba Bashar al-Assad da masu adawa dashi, sunyi amfani da makamai don kai hare-hare ga abokan hamayya.

Karin bayani