An yanke wa Mubarak hukuncin daurin rai-da-rai

mubarak Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mubarak akan hanyarsa ta komawa gidan kaso

Kotu a birnin Alkahira na Masar ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai a kan tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak.

An same shi ne da laifin hadin baki wajen kisan masu zanga-zanga a lokacin da aka yi boren da ya hambarar da shi daga kujerar mulki a bara.

Mai shari'a Ahmad Rif'at ne ya bayyana hukuncin, "Kotu ta yanke hukunci a gaban wadanda aka gurfanar, in banda wanda aka gurfanar na biyu wanda shi hukuncinsa na bayan-ido ne.

Mai shari'ar ya kara da cewar, "Na farko an yanke hukuncin daurin rai-da-rai a kan Muhammad Husni As Sayyid Mubarak, bisa hadin baki wajen".

Har ila yau, alkalin kotun, ya bayyana cewar al'ummar kasar Masar, sun sha bakar azaba a cikin shekaru talatin din da Mubarak yayi akan mulki, a don haka yana ganin cewar hukuncin da aka yankewa tsohon shugaban ya yi dai dai.

Sannan kuma alkalin ya sanarda hukuncin daurin rai da rai akan tsohon ministan harkokin cikin gidan Masar, Habib Al Adly.

A ita wannan kotun, an wanke tsohon shugaban da 'ya'yansa guda biyu Ala da Jamal daga wata tuhuma ta cin hanci da rashawa da ake yi masu.

Sai dai 'ya'yan na Mubarak za su ci gaba da kasancewa a jarun a kan wata tuhumar cuku-cukun bayanan sirri na kasuwar hannun jari.

An kuma sami wasu shugabannin 'yan sanda da laifin kisan masu zanga-zanga a boren na bara a kan tsohon shugaban.

Wannan hukuncin dai ya nuna cewar tsohon shugaban na Masar, Hosni Mubarak mai shekaru 84 wanda ke fama da ciwon zuciya zai shafe sai rayuwarsa ne a gidan kurkuku na Tura.

Karin bayani