An saki dan Italiyar da aka yi garkuwa da shi a Najeriya

Garkuwa da mutane a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Garkuwa da mutane a Najeriya

Rahotanni a Najeriya na cewa an saki wani injiniya dan kasar Italiyan nan da wasu suka sace a farkon wannan makon a jihar Kwara dake arewacin kasar.

Ministan harkokin wajen Italiya Gulio Terzi da ya tabbatar da sakin mutumin, ya yabawa hukumomin Najeriyar kan hadin kan da suka bayar wajen samun nasarar sakin dan kasar tasa, kwana daya da kisan wani Injiniyan dan kasar Jamus da aka sace tun watan Janairu a Kano.

Wannan lamari dai ya faru ne watanni biyu bayan kisan wani dan kasar Italiyar tare da abokin aikin sa dan Birtaniya , a yayin yunkurin kubutar dasu a Sokoto dake arewacin Najeriyar.