Amurka za ta tura jiragen yaki yankin Asia da Pacific.

Sakataren tsaron Amurka Leon Panetta Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sakataren tsaron Amurka Leon Panetta

Sakataren harkokin tsaron Amurka Leon Panetta yace Amurkar za ta tura jiragen ruwan yakinta yankin Asia da Pacific nan da shekara ta 2020.

Mr Panetta ya shaidawa taron harkokin tsaron yankin a kasar Singapore cewar kashi 60 bisa dari na jiragen ruwan Amurkar zasu kasance a yankin Pacific.

Wannan mataki na daya daga cikin sabbin dabarun harkokin tsaro na duniya da shugaba Obama ya tsara a farkon wannan shekarar.

Mr Panetta yace hakan ba yana nufin kawo barazana ga kasar China ba ne kamar yadda wasu ke tunani.