Jirgin sama yayi hatsari a Ghana.

Jirgin saman kamfanin Allied Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin saman kamfanin Allied

Wani jirgin daukar kaya ya yi hatsari a kusa da filin saukar jiragen sama na Accra, babban birnin kasar Ghana.

Rahotanni sun ce jirgin ya taso ne daga Najeriya kan hanyarsa ta zuwa kasar Ghana, kuma ya gamu da hatsarin ne sakamakon rashin kyaun yanayi saboda ruwa da iska da ake yi a lokacin.

Jirgin ya bugi wata motar bas ne makare da fasinjoji a daidai lokacin da yake kokarin sauka,wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane goma dake cikin motar bus din, yayin da ma'aikatan jirgin su hudu suka tsira da rayukansu.

Jirgin dai mallakar wani kamfanin zirga-zirgar jiragen sama ne a Najeriya mai suna Allied Air.