Yan kasar Masar na ci gaba da zanga zanga.

Masu zanga zanga a dandalin Tahir Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga zanga a dandalin Tahir

Dubun dubatar yan kasar Masar ne ke gudanar da zanga-zanga a dandalin Tahrir dake birnin Alkahira, kan hukuncin da aka yankewa tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak da wasu mukarraban sa.

An dai yankewa Mubarak da tsohon Ministan harkokin cikin gidansa Habib al- Adly hukuncin daurin rai da rai sakamakon samun su da aka yi da laifin haddasa kisan daruruwan masu zanga-zanga a rikicin da ya faru cikin shekarar da ta gabata.

Manyan kwamandojin 'yansanda shida ne kotun ta sallama, yayin da aka wanke Mubarak da dansa daga zargin cin hanci da rashawa.

Masu zanga-zangar sun bukaci a yankewa wadanda ake tuhumar ne hukuncin kisa .Don haka kungiyoyin siyasa suka yi kira ga jama'a su fito kwansu da kwarkwata domin yin Allah wadai da abinda suka ce rashin adalci a shari'ar.