BBC navigation

Hukumomi a Nigeria sun dakatar da lasisin Dana Air

An sabunta: 4 ga Yuni, 2012 - An wallafa a 15:18 GMT

Hukumomi a Nigeria sun dakatar da lasisin kamfanin Dana Air bayanda wani jirgin kamfanin me dauke da fasijojin ya fadi a Lagos inda mutane akalla dari hamsin da tara sun hallaka.

Kakakin hukumar Sam Adurogboye yace sun dakatar da lasisin kamfanin ne bayan hadarin jirgin sama.

Ya ce zasu yi bincike akan yadda kamfanin ke gudanar da ayukansa

A wani labari Majalisar wakilai ta kasar ta bukaci a dakatar da shugaban hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta Nigeria Mr Harold Demuren.


Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da masu aikin ceto suka ce kawo yanzu sun gano gawarwawwki 150.

A yau ne dai aka shiga rana ta biyu ta zaman makokin da ake yi a kasar sakamakon asarar rayukan da aka yi a hadarin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.