Gasar turai ta 2012: Gary Cahill da Rio Ferdinand ba za su buga ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cocin Ingila Roy Hodgson

Gasar EUROta bana: Gary Cahill da Rio Ferdinand ba za su buga ba

An zargi Roy Hodgson da rashin mutunta Rio Ferdinand saboda ya ki sa dan wasan baya , a cikin jerin yan kwallon kafa da zasu yi wasa a gasar Euro ta shekerar 2012 duk da cewa Gary Cahill ya sami rauni.

Cahill, me shekaru 26, an cire sunansa biyo bayan raunin da ya samu a kashin muka-mukinshi bayan da su ka ci karo da me tsaron gida Joe Hart a wasan sada zumunta inda su ka sami galaba akan kasar Belgium a ranar asabar.

Martin Kelly da ke taka leda a klub din Liverpool shi ne zai maye gurbinsa.

"Wanan rashin girmamawace. Ya na son ya taka leda" inji Jamie Moralee wanda shi ne wakilin Ferdinand.

Ferdinand wanda ya taba rike mukamin kyaptin, me shekaru talatin da uku ya takawa kasarsa leda sau 81 sai dai ba ya cikin jerin sunnayen yan wasa da cocin ingila ya fitar.

Cocin Ingila Hodgson yace ya dau wanan matakin ne bisa dalilan kwallon kafa kuma yayinda Terry ke shirin gurfana a gaban sharia a watan yuli me zuwa game da tuhumar da ake yi masa na aiwatar da kalaman batanci ga dan uwan Ferdinand watau Anton.

Sai dai Terry ya musanta zargin.