An kafa kwamiti kan kiyaye hadurran jiragen sama a Nijeriya

jirgin Dana Air da ya fadi a Lagos
Image caption jirgin Dana Air da ya fadi a Lagos

Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamitin da zai duba yadda jiragen sama ke gudanar da harkokin sufuri a matakin cikin gida.

Hakazalika an bukaci kwamitin da ya yi nazarin yadda hukumomin da ke sa-ido a kan harkokin sufurin jiragen saman ke tafiyar da ayyukansu a kasar, tare da bada shawarwari a kan yadda za su inganta su.

Gwamnatin Najeriyar ta dauki wannan matakin ne bayan wani hadarin da jirgin saman kamfanin Dana Air ya yi, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum dari da hamsin a ranar Lahadin da ta gabata.

A waje daya kuma 'yan uwan wadanda suka rasu a hadarin jirgin sun gudanar da wata zanga zangar lumana a Lagos, domin nuna korafinsu kan abinda suka kira, irin jan jikin da ake yi wajen tantance gawarwakin 'yan uwansu da suke so a mika ma su, domin yi masu sutura.

Haka nan wani darakta a kampanin Dana Air, Alh Francis Ogoro ya bayyana takaicin kampanin nasu game da aukuwar wannan hadari, tare da nuna alhini game a asarar rayukan da aka yi.

Ya ce suna ci gaba da bincike, a yunkurin biyan diyya ga wadanda suka rasu a hadarin jirgin saman.

Karin bayani