Moody's ta rage karfin wasu bankunan Jamus

Alamar bankin Commerzbank na Jamus Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alamar bankin Commerzbank na Jamus

Cibiyar kimanta karfin biyan bashi ta Moody's ta rage darajar karfin biyan bashi na bankunan Jamus guda shidda, ciki har da banki na biyu mafi girma a kasar, wato Commerzbank.

Cibiyar ta Moody's ta ce ta yanke shawarar daukar wannan mataki ne ganin karin hadarin da matsalar tattalin arzikin kasashen da ke amfani da kudin Euro ka iya haifarwa.

Wakilin BBC ya ce rage darajar bankunan ya nuna cewa a tunanin Moody's idan matsalar kasashe masu amfani da kudin Euro ta kara kazancewa, to Jamus ma za ta shiga matsala.

Karin bayani