Boko Haram ta musanta shiga taron sulhu

Malam Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Malam Abubakar Shekau

Kungiyar Jama'atu Ahlissuna Liddaawati wal Jihad, da aka fi sani da suna Boko Haram, ta musanta rahotannin dake cewa an fara wata tattaunawa tsakaninta da gwamnati da nufin yin sulhu.

Cikin wani sakon email mai dauke da sunan Abul Qaqa, kungiyar ta ce ya zama wajibi ta maida martani kan rahotannin dake cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi na shiga tsakaninta da gwamnati,tana mai cewa babu kanshin gaskiya a rahotannin.

Kungiyar ta yi kira ga Sheikh Dahiru Bauchi da cewa , " ya ja girmansa, kada ya bari wasu su yaudare shi."

Tun farko dai Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shaidawa BBC cewar lallai akwai tattaunawar da yake kokarin jagoranta tsakanin gwamnatin da 'yan kungiyar.

Ita dai kungiyar ta ce rabonta da shiga wata tattaunawa da hukumomin Nijeriya, tun wadda ta ruguje karkashin jagorancin Dr Datti Ahmad.

Yayinda wasu suka fara jinjina ma yunkurin sulhun, domin kawo karshen tashin hankalin da yake sanadiyar mutuwar daruruwan jama'a a Nijeriya, bisa dukkan alamu murnar irin wadannan mutane zata koma ciki kenan a yanzu.

Karin bayani