'Mun kashe 'yan Boko Haram fiye da goma'

Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Sheikh Abubakar Shekau

Rundunar da ke aikin tabbatar da tsaro a jihar Barnon Najeriya ta ce ta kashe 'yan kungiyar Ahlussuna Lidda'awati Wal jihad da aka fi sani Boko Haram fiye da goma a wani bata-kashi da aka shafe sa'oi da dama ana yi a birnin Maiduguri ranar Talata.

Wani jami'i a rundunar, Kaptin Victor Ebhaleme, ya ce lamarin ya faru ne a unguwar Shehuri da ke tsakiyar birnin.

Ya kara da cewa rundunarsa ta yi nasarar kwato makamai a wasu wuraren da 'yan kungiyar ke zama a birnin na Maiduguri.

Hakan na faruwa ne a lokacin da rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kashe wani tsohon mataimakin Supeto Janar na 'yan sandan kasar, DIG Abubakar Saleh Ningi, ranar Talata da yamma.

A cewar rundunar 'yan sandan, wasu 'yan bindiga ne suka budewa motar da ke dauke da DIG Sale Ningi da dogarinsa, da kuma matukin motarsa wuta a rukunin masana'antu da ke yankin Sauna a gabashin birnin.

Sasantawa da 'yan Boko Haram

A wani bangaren kuma, fitaccen malamin addinin Islaman nan da ke Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana cewa yana jagorantar wani shirin sulhu tsakanin gwamnati da 'yan kungiyar Boko Haram.

Sheikh Bauchi ya bayyana wa manema labarai a garin Bauchi cewa bangarorin biyu sun yarda su ci gaba da tattaunawa yayin da yake jagorantar shiga tsakani bisa wasu sharudda da bangarorin biyu suka shimfida.

A baya dai tattaunawa tsakanin hukumomin Najeriyar da kuma 'yan kungiyar ta Boko Haram ta wargaje bayan da masu shiga tsakani suka zargi gwamnati da yin kafar-ungulu ga shirin sulhun, zargin da gwamnatin ta sha musantawa.

Karin bayani