Annan ya koka kan rikicin Syria

motar wakilan majalisar dinkin duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption motar wakilan majalisar dinkin duniya

Wakilin kasashen duniya a Syria, Kofi Annan ya fadawa babban taron MDD cewa lokaci ya yi da za a yiwa gwamnatin Syriar barazanar daukar tsauraran matakai a kanta, muddin ba ta dakatar da hare-haren da ake kai wa a kan fararen hula ba.

Mr Annan ya bayyana takaicinsa matuka game da rahotannin kisan gillar da aka yi wa mutane kusan tamanin(80) a kauyen Qubeir dake lardin Hama.

Mr Annan ya amsa cewa irin wannan tashin hankali ya nuna karara cewa shirinsa na wanzar da zaman lafiya a kasar ta Syria, ba ya aiki .

Sai dai Rasha da China , wadanda ke mara wa Syriar baya, sun ce za su yi adawa da duk wani kira na a tura sojojin kasashen waje zuwa kasar ta Syria.

A halin da ake ciki kuma, shugaban Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Syria, ya ce an hana jami'an dake sa ido a Syriar zuwa kauyen na Qubeir.

Sai dai wani labari da muka samu yanzun nan , ya ce gidan talabijin din Syria ya ce tawagar jami'an Majalisar Dinkin Duniyar dake sa ido a kasar sun shiga kauyen na Qubeir.

Karin bayani