An kashe fiye da mutane 70 a Syria

Masu fafutika 'yan adawa a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu fafutika 'yan adawa a Syria

Masu fafutika na bangaren adawa a Syria sun zargi dakarun sa-kai masu goyon bayan gwamnati da aikata wani sabon kisan-gilla a kasar

Wasu rahotanni dai sun ce mutane fiye da 70 ne aka hallaka, yayinda dakarun sa-kan suka kai hari a kan kauyen Qubeir dake lardin Hama.

A halin da ake ciki kuma, shugaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Syria ya ce an hana jami'an dake sa ido a Syriar zuwa kauyen na Qubeir.

Kakakin ofishin, Sausan Ghosheh, tace: "Har ya zuwa yanzu, jami'anmu dake sa-ido ba su samu damar cimma kauyen ba, domin kuwa sojojin gwamnati sun tare su a wuraren binciken ababen hawa.

"Haka kuma mazauna kauyen na bugo mana waya, suna fada mana cewa rayuwar jami'anmu na fuskantar bazarana, idan suka shiga kauyen".

Sai dai wani labari da muka samu yanzun nan ya ce gidan talabijin din Syria ya ce tawagar jami'an Majalisar Dinkin Duniya dake sa-ido a kasar sun shiga kauyen na Qubeir.

'Yan ta'adda

Gwamnatin Syrian dai ta dora alhakin kashe-kashen da aka yi a kauyen na Qubeir, a kan wadanda ta kira kungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da makamai.

Tace mazauna kauyen sun nemi sojoji ne su shiga kauyen domin maido da doka da oda.

Gwamnatin ta ce 'yan tawaye ne suka kai harin da nufin janyo kasashen duniya su yi katsalandan a kasar.

Karin bayani