An kai wa shedkwatar rundunar yan sanda hari a Maiduguri

Rahotani daga birnin maiduguri a jihar Borno sun ce wani dan kunar bakin wake ya kaiwa shedkwatar yan sanda hari.

Rahotanin sun kuma ce bam ya tashi a unguwar gidan dambe dake tsakiyar birnin Maiduguri.

Da safiyar yau ne aka dana bam din a unguwar kuma ya tashi ne a lokacin wani mutum ya je taba bam din a cewar rahotanin.

Kawo yanzu dai ba'a san yawan mutanen da suka rasu da kuma wadanda suka sami raunuka ba kuma ba bu wata kungiyar da ta dau alhakin kai hare haren.

Ko da yake a baya kungiyar ahlus sunna liddaa'awati wal jihad da aka fi sani da boko haram ta ringa ikararin cewa ita ce ta kai hare haren.