'Yan tawayen Mali na gwabza kazamin fada

Yan tawayen Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yan tawayen Mali

An samun rahoton cewa Abzinawa 'yan tawaye da mayaka masu kishin Islama sun gabza fada a arewacin Mali, mako daya bayan lalacewar kawancen da suka yi.

Shedu sunce bangarorin biyu sun budewa juna wuta, da makamai masu sarrafa kansu, kusa da birnin Kidal.

Babu rahoto akan cewa ko an kashe mutane ko an jima wasu raunuka.

A ranarJuma'ar da ta gabata dai kungiyar Abzinawa, MNLA, wanda tace bata da alaka da wani addini, taki amincewa da bukatar 'yan kungiyar ma'abuta Islaman cewa a kafa shari'ar Musulunci a yankin.

Karin bayani