Rahoton UNICEF kan mace macen yara a duniya

kananan yara a Afrika Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption kananan yara a Afrika

Wani rahoto da asusu kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya, wato UNICEF, ya fitar a yau Jumma'a, ya nuna cewa cutar huhu ta nimoniya da gudawa suna cikin manyan cututtukan da ke haddasa mutuwar yara kanana a kasashe daban-daban na duniya.

Kimanin yara miliyan biyu ne ke mutuwa a duniya a kowace shekara, sakamakon cututtukan.

Rahoton ya ce kimanin rabin mace-macen yara kananan yana aukuwa ne a wasu kasashe biyar, ciki kuwa har da Najeriya.

Ta'adin da wadannan cututtuka biyu suke yi kuwa, ya zarta na cutar nan ta AIDS ko SIDA, mai karya garkuwar jiki, da ta zazzabin cizon sauro a duniya.

Rahoton ya ce shayar da jarirai nonon uwa zalla na tsawon watanni shidda bayan haihuwa zai taimaka gaya, wajen rage kamuwa da cututtukan.

Karin bayani