Bankunan Turai na bukatar tallafi, inji Lagarde

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lagarde

Manajan Darakta ta Asusun bada lamuni na duniya ta ce farfado da karfin bankunan Turai na da matukar muhimmanci wurin bunkasa tattalin arzikin duniya.

Da ta ke jawabi a New York, Christine Lagarde ta ce shekaru biyar bayan shiga cikin rikicin tattalin arziki, har yanzu ana samun matsaloli a fannin hada-hadar kudi na nahiyar Turai.

A na sa bangaren shugaban Amurka Barak Obama ya bukaci kasashen Turai da su taimakawa bankunan da ke barazanar durkushe da karin jari.

Farfado da tattalin arzikin yankin nahiyar turai ka iya rage illolin da tsuke bakin aljihun gwamnatoci ke haifarwa

Karin bayani