An kama wasu ma'aikatan ICC a Libya

Mai shigar da kara na kotun ICC Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mai shigar da kara na kotun ICC

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ce an tsare ma'akaitanta hudu a Libya, inda suka je don su gana da Saiful Islam, dan tsohon shugaban kasar, marigayi Kanar Ghaddafi.

Shugaban kotun yace ya damu matuka akan halin da mutanen ke ciki yana mai kira ga hukumomin Libyar da su sake su ba tare da wani bata lokaci ba.

Tun farko an bada labarin cewa an tsare wata lauyar kotun bayan ta yi yunkurin bawa Saiful Islam din wasu takardun da ke kunshe da bayanan sirri.

Ahmed Ajehani wani lauyna a Libyan yace lokacin da ta ziyarci Saiful Islam, lauyar tayi kokarin mika masa wasu takardu da tace ya sa hannu.

Takardun sun fito ne daga wasu mutane daga wajen kasar ciki har da Mohammed Ismail wani tsohon na hannun daman Saiful Islam din.

Karin bayani