Bankunan Spain sun shiga tsaka maiyuwa

Bankunan Spain Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bankunan Spain

Ministan tattalin arzikin Spain zai yi wata ganawa idan anjima da sauran ministocin tattalin arzikin kasashen Turai inda ake saran zai bukaci taimakon gaggawa don ceto bankunan kasarsa.

Hukumar bada lamuni ta duniya ta ce bankunan Spain na bukatar a kalla dala biliyan 50.

Kuma yanzu haka gwamnatin Spain din tace tana nazarin wannan rohoton hukumar.

Waklin BBC a Madrid yace kasar na fuskantar matsin lamba na ta dauki wani matakin gaggawa da zai taimakawa bankunan kasar, wadanda bashi ya yiwa katutu.

A waje daya kuma shugaban babban bankin kasar Jamus ya yi kira ga Spain da ta yi amfani da kudadan asusun ceto tattalin arzukin kasashen tarayyar turai.

Karin bayani