Ana ci gaba da kashe kashe a Syria

An kai hari a wasu biranan Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kai hari a wasu biranan Syria

'Yan adawa a Syria sun ce a kalla fararan hula 17 ne dakarun gwamnati suka hallaka a daren jiya a birnin Deraa.

An kuma rawaito cewa an kashe wasu mutane 40 a wata karawa da akayi ranar juma'a a sassan kasar dadama.

Wani mazaunin birnin ya shaidawa BBC cewa lamarin wani babban bala'i ne.

Har yanzu ana ta luguden wuta kuma ana ta jefa rokoki akan birnin, wanda shi ne inda aka fara yujin juya hali a kasar.

Wani wakilin BBC a Damascus ya ga hayaki ya turnike a wajen babban birnin kasar ta Syria, ya kuma ce akwai rahotanni dake cewa an kai hari kan wata tashar wutar lantarki.

Har yanzu tawagar masu sa ido ta Majalisar Dinkin Duniya na kokarin tabbatar da ainahin abin da ya faru a kauyen Qubeir, inda ake zargin mayakan sakai dake goyan bayan gwamnati da aikata kisan kiyashi na kimanin mutane tamanin ranar laraba.

Karin bayani