Liberia ta rufe iyakar ta da Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gawar sojin UN da aka kashe

Liberia ta rufe iyakarta da Ivory Coast kwana guda bayan da aka kashe sojin majalisar dinkin duniya bakwai da farar hula da dama a wani samame da aka kai a iyakar Ivory Coast.

Jami'in yada labarai na Liberia, Lewis Brown yace ana cigaba da binciken gano daga inda maharan suka fito amma a yanzu an rufe iyakar kuma za'a tura dakarun Liberia zuwa yankin.

Mahukuntan Ivory Coast dai na zargin mayakan da ke da sansani a Liberia ne da kai harin.

Harin dai shi ne mafi muni tun farkon zuwan dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya shekaru takwas da suka wuce.

Karin bayani