ICC ta ja kunnen Libya kan ma'aikatan ta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Libya

kotun laifuffuka ta duniya wato International Crminal Court (ICC) ta ce an garke wasu ma'aikatan ta guda hudu a Libya inda suka isa kasar don su gana da dan marigayi Ghaddafi, Seif al Islam.

Shugaban kotun ya ce yana matukar damuwa kan lafiyar ma'aikatan kuma ya yi kira da a sake su da gaggawa.

Kotun da kuma gwamnatin Libya dukkanin su na son su gurfanar da Seif Al Islam ne a gaban kotu bisa zargin da ake masa na rawar da ya taka kan murkushe masu bore abunda ya habbarar da gwamnatin Ghaddafi.

Sai dai gwamnatin na son a yi masa sharia a cikin gida ita kuwa kotun na son yin shariar ne a wajen kasar.

Karin bayani