Ana gwabza fada a kudancin Libya

Ana gwamba fada a Libya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana gwamba fada a Libya

An shiga rana ta biyu a Libya a karawar da akeyi tsakanin dakarun gwamnati da mayakan kabilu a garin Kufra.

A kalla mutane goma sha shida ne aka kashe a lamarin yayin da aka jikkata wasu goma sha tara.

Tashin hankalin baya bayan nan ya faru ne jiya lokacin da mayakan kabilun suka hari wani wurin binciken ababen hawa da tankunan yaki.

Sai dai kuma wakilan kabilar Tabu sunce dakarun gwamnati ne suka fara kai masu hari.

Har yanzu ana ta musayar wuta a garin na Kufra dake kudancin Libyar.

Karin bayani