Peru ta gano helicopter da ya fadi

Hakkin mallakar hoto w
Image caption helicoptan Peru da ya fadi

'Yan sanda a Peru sun gano wani helicopter da ya fadi ranar Laraba, ya hallaka gaba dayan mutane goma sha hudun da ya dauko.

Mafi yawan mutanen 'yan kasar Koriya ta kudu ne.

An gano helikoptan ne akan wani tsauni mai tudun kusan kilomita biyar.

Dusar kankara da ta mamaye wurin ta kawo tarnaki ga kokarin ceto wadanda hatsarin ya rutsa da su.

Karin bayani