Spain ta samu goyon baya kan ceto Bankuna

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Luis De Guindos, Ministan kudi na Spain

Matakin da kasar Spain da dauka na bukatar lamuni wanda zai kai dala biliyan 125 daga yankin Turai don ceto bankunan kasar; ya samu goyon baya sosai.

Asusu bada lamuni na duniya ya ce kudaden ceton sun isa su dawo da martabar tsarin bankunan kasar ta Spain.

Haka ma dai Amurka ta yi marhabun da matakan da aka dauka a matsayin wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin yankin turai.

Bashi ya yi wa Bankunan kasar katutu.

Karin bayani