Wakilan kotun laifuffuka sun isa Tripoli

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption ICC Libya

Wakilan kotun hukunta masu manyan laifuffuka ta duniya, ICC, sun isa Tripoli, babban birnin Libya.

Kotun ICC din dai na kokarin ganin an sako ma'aikatan kotun guda hudu da aka tsare su a garin Zintan.

Mahukuntan Libya sun ce daya daga cikin wadanda aka tsare ta yi kokarin baiwa Saiful Islam Gaddafi dan marigayi shugaban Libya, wadansu bayanai da ke da hatsari ga zaman lafiyar Libya.

Kotun ta ICC ta bukaci a sake mutanen nan take.

Karin bayani