Barayi sun kashe mutane sama da ashirin a Zamfara

Jami'an tsaro a Nijeriya
Image caption Jami'an tsaro a Nijeriya

Rahotanni daga jahar Zamfara, a arewacin Najeriya sun ce mutane akalla ashirin da uku ne suka hallaka, lokacin da wani gungun mutane dauke bindigogi suka kai wa wasu kauyuka hari da sanyin safiyar yau Litinin.

Yanzu haka kuma wasu mutanen bakwai na karbar magani a asibiti bayan maharan da ake jin 'yan fashi da makami ne sun afkawa kauyukan Dangulbi da sabuwar kasuwa Guru.

Ana dai jin cewar harin na ramuwar gayya ne kan yadda aka ce 'yan banga a kauyukan suna fatattakar 'yan fashin da ke addabar yankunan, inda a wasu lokuttan suke karkashe su.

Ko a watannin baya, irin wadannan mahara sun kai hare hare irin wannan inda suka halaka mutane da dama.

A yanzu rahotanni na cewa al'amurra sun lafa, amma babu abin da ke nuna cewa an kama koda mutum guda game da hare haren.

Karin bayani