Wasu kasashe 7 sun tsira daga takunkumi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Barack Obama

Kasar Amurka ta kara cire wasu kasashe bakwai daga cikin jerin sunayen kasashen da zata iya kakabawa takunkumi kan sayen mai daga Iran.

Kasashen dai sun hada da Indiya da koriya ta Kudu da turkiyya da Malasiya da Afrika ta Kudu da Sri-lanka da kuma Taiwan.

Dama dai an cire wasu kasashe goma dake cikin kungiyar tarayyar turai da kuma Japan daga jerin sunayen kasashen, amma kasar Sin zata iya fuskantar takunkumin.

Kasar Amurkar dai tana son dakile yawan kudaden shigar da Iran ke samu daga sayar da danyan mai domin tilasta mata jingine shirin ta na makamashin nukiya.

Karin bayani