Mun shirya zuwa yaki a Mali - Issoufou

issoufou
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar ya ce a shirye yake ya je yaki a Mali mai makwabtaka da kasarsa domin warware takaddamar da ake fama da ita a can.

Da yake magana a London jim kadan kafin ya gana da Pirayi Ministan Birtaniya, David Cameron, Shugaba Issoufou ya ce akwai kawancen 'yan ta'adda a arewacin Mali.

A cewarsa zai gabatar da wani kuduri akan haka gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya a New York a ranar Laraba mai zuwa.

Ya kara da cewar akwai wasu sansanoni a Mali da 'yan ta'adda daga Afghanistan da Pakistan suke horradda mutane a wajen.