Nijer na kira da saka hannun jari a kasar

Image caption mahmadou issoufou

Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar, Alhaji Mahamadou Isoufou ya fara wata ziyarar aiki a Burtaniya.

A lokacin ziyarar ta kwanaki hudu, shugaban na Nijar zai gana da shugabannin siyasa na Burtaniya, sannan zai halarci wani babban taro kan batun saka jari a kasar ta Nijar, wanda za'a bude a ranar Alhamis mai zuwa.

Burtaniya da Amurka ne dai suka shirya wannan taron domin kwadaita wa masu zuba jari na kasashensu su je su zuba jari a Nijar din.

Kasar Nijer din dai na da maadanai irinsu Uranium da wasu maadanai wanda za'a iya saka hannun jari don bunkasar harkokin da kuma kara tattalin arzikin kasar.

Karin bayani