'Yanbindiga sun kashe mutane uku a Bukur na Jihar Pilato

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga jihar Filato na cewa wasu 'yan bindiga sun bude wuta kan masu sana'ar sayar da tsaffin karafa a garin Bukur dake kimanin kilomita arba'in kudu da Jos babban birnin jihar.

Yan bindigar wadanda suka tsaya a gefen titi da motarsu sun yi ta harbin kan mai tsautsayi inda kuma suka kashe mutane uku sannan suka sulale.

Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da ake arangama tsakanin jami'an tsaro da matasa yan acaba a cikin birnin Jos.

Sai dai hukumomi sun bayyana cewa babu wata alaka tsakanin lamuran biyu.

Harin da yan bindigar suka kai dai ya haifar da matukar zaman dardar a garin wanda yana daya daga cikin wuraren da ke fama da rikicin kabilanci da na addini a jihar ta Pilato.

Sakamakon sa kuma yan kasuwa sun rufe shagunansu saboda fargabar abinda kaje ya dawo.

Karin bayani