Majalisar wakilai ta dakatar da Faruk Lawal

 Hon Faruk Lawal Hakkin mallakar hoto google
Image caption An zargi Faruk Lawal da karbar toshiyar baki, sai dai ya musanta

Majalisar wakilan Najeriya ta dakatar da Hon Faruk Lawal daga mukaminsa na shugabancin kwamitin da ya binciki badakalar biyan kudaden tallafin man fetur.

Wannan yana cikin wani bangare na matakin da Majalisar ta dauka a zaman gaggawar da ta fara a ranar Juma'a domin duba zargin karbar toshiyar baki da aka baiwa Faruk Lawal da kuma Sakataren kwamitin Hon. Boniface Emenalo.

Majalisar ta kuma nemi kwamitinta na da'a da ya yi bincike kan Emenalo domin daukar matakin da ya dace a kansa.

Majalisar ta kuma sake duba matsayar da ta dauka a ranar 24 ga watan Afrilu, na wanke kamfanin Zenon Petroleum and Gas and Synopsis Enterprises daga hannu a badakalar tallafin man.

A halin yanzu dai Majalisar na ci gaba da tattaunawa kan wannan batu.

Tun da farko an zargi Zenon Petroleum and Gas, mallakin Femi Otedola da karbar dala 232,975,385.13 domin shigowa da man fetur, sai dai basu shigo da man ba.