An kai gawar sojojin Nijar gida daga daga Cote D'Ivoire

Gawar sojin Majalisar dinkin duniya da aka kashe a Cote D'Ivoire Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gawar sojin Majalisar dinkin duniya da aka kashe a Cote D'Ivoire

A jamhuriyar Nijar an kai gawarwakin sojojin nan bakwai 'yan kasar da aka kashe a kasar Cote d'Ivoire makon jiya

Gobe da safe ne kuma za a yi jana'izatsu a yamai.

Sojojin dai sun rasa rayukansu ne a wani hari da ake zaton yan tawaye a kasar ta Cote d'Ivoire ne suka kai masu, a kusa da kan iyaka da Liberia.

Suna kuma aikin na kyautata zaman lafiya a kasar Cote d'Ivoire sakamakon rikicin tawaye da na siyasar da ta shiga shekarun baya.

Karin bayani