Syria ta kwato garin al-Haffa

Hakkin mallakar hoto AP

Dakarun gwamnatin Syria sun kwace garin nan mai tsaunuka inda suka shafe makon da ya gabata suna yiwa sojojin 'yan tawaye kawanya.

An ba da rahoton cewa cikin daren Talata ne mayakan 'yan tawayen suka janye daga garin na al-Haffa.

Bangarorin biyu sun zargi juna da shirin aikata wani sabon kisan kiyashi a garin, irin wanda aka aikata a Houla da Qubair.

An kuma ba da rahoton tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar ta Syria, ciki har da birnin Homs da garuruwan dake arewa da shi.

Wani hoton bidiyo da aka saka a intanet ya nuna yadda aka ce an yi ta luguden wuta a kan birnin na Homs.

'Yan adawa masu fafutuka sun ce akalla mutane arba'in sun rasa rayukansu a fadin kasar, yayinda gwamnati ta ce ta yi jana'izar sojojinta kusan talatin.

Karin bayani