Wani ya cinnawa kotu wuta a Funtua

nigeria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga garin Funtua a jihar Katsinan Najeriya na cewa,wani matashi ya sa wa wata kotu wuta sakamakon bakin cikin hukuncin da kotun ta yi masa.

Bincike dai ya nuna cewa kotun, wadda ta daukaka kara ce, ta taba yi masa shari'a tsakaninsa da wata masoyiyarsa, amma bai ji dadin hukuncin ba.

Wutar dai ta kona wasu muhimman sassan kotun, ciki har da ofishin magatakarda da na Alkali.

Kamar yadda bincike ya nuna, ana zargin zakara ya bai wa matashin sa'a ne, kasancewar tun da jijjifin safiyar yau din nan ya sammaka zuwa kotun, wadda ta daukaka kara ce ta Shari'ar Addinin musulunci da ke garin Funtua, dauke da guzurin man fetur da ke cikin wani galon, kuma da isarsa bai tsaya wata-wata ba sai ya duba wasu sassan kotun ya yayyafe da man fetur din, kana ya banka wa kotun wuta.

Wadanda lamarin ya auku a kan idanunsu dai sun ce an taki sa'a duk kuwa da cewa wutar ta yi wa kotun illa sosai, kasancewar ba a rasa rai ba saboda a lokacin babu mutane a masu yawa a kotun sai mai gadinta, wanda shi ma ya yi ta neman dauki ganin lamarin ya fi karfinsa.

Karin bayani