An zargi Syria da aikata laifukan yaki

Hakkin mallakar hoto na
Image caption Tashin hankali a Syria

A wani sabon rahoto da kungiyar kare hakkin dan-adam Amnesty International ta fitar, an zargi gwamnatin Syria da aikata laifukkan yaki da na cin zarafin bil-adama.

Kungiyar Amnesty ta ce masu binciken ta sun zan ta da mutane fiye da dari biyu mazauna garuruwa da kauyukan Syria tun a tsakiyar watan Aprilu.

Amnesty ta zargi gwamnatin da laifin aiwatar da manufar kisan kaare-dangi a wasu yankuna inda ta rinka kashewa da ganawa farar hula azaba da harbe dabbobi da kone amfanin gona da gidaje.

A garin Aleppo, masu binciken na kungiyar Amnesty sun ga sojojin gwamnatin Syria da sojin sa kai dake rufa musu baya suna budewa wani taron gangami na lumana wuta.